<?xml version="1.0" encoding="UTF-8"?><song><author>Hughes, John (1873-1932), Williams, William (1717-1791)</author>
<title>Ka Bishe Ni, Ya Jehovah LW204</title>
<lyrics>[V1]
 1) Ka bishe ni, ya Jehovah,
 Ni baƙo ne a duniyan nan.
 Ni rarrauna, kai Mai Iko,
 Riƙe ni da hannunka.
 Ka cishe ni, ka cishe ni,
 Da gutasan nan mai rai.
 Da gurasan nan mai rai.

[V2]
 2) Buɗe mini, ya Mai Ceto,
 Maƃulƃula masu rai.
 Ka bishe ni da idonka,
 Har an kai ni a wurinka,
 Taimakona, taimakona,
 Kai ka zama ƙarfina.
 Kai ka zama ƙarfina.

[V3]
 3) In na taka kwarin mutuwa,
 Kau da dukan tsorona,
 Tokare ni da hannunka,
 Kai ni can a gidanka.
 Waƙar yabo, waƙar yabo
 Taka ce har abada.
 Taka ce har abada.</lyrics>
<hymn_number>204</hymn_number>
</song>